Laraba 24 Yuni 2026 - 17:12
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (44) | Matsayin Intizar A Al'adar Shi'a (Kashi na Uku)

Hauza: Intizar yana nufin sa ido da jiran makoma mai kunshe da dukkan siffofin al'umma ta Ubangiji, wanda tabbataccen misalinsa guda daya ne kawai, wato zamanin mulkin wakilin Ubangiji na karshe.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin bahasin Mahdawiya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimomi masu alaka da Imamin Zamani (Allah ya gaggauta bayyanarsa), zuwa gare ku masana masu daraja.

A kashi na baya, an bayyana cewa hadisan da aka ambaci "Jira" (Intizar) a cikinsu sun kasu kashi biyu.

Kashi na biyu na hadisan ya tattauna ne akan "Jiran samun sauki (Faraj) a ma'anarsa ta musamman", wanda za mu yi ishara da shi a wannan kashi:

Jiran Samun Sauki (Faraj) a Ma'anarsa Ta Musamman

A cikin wannan ma'ana, jira yana nufin sa ido da jiran makoma mai kunshe da dukkan siffofin al'umma ta Ubangiji, wanda tabbataccen misalinsa guda daya ne tilo, wato zamanin mulkin wakilin Ubangiji na karshe, wato tsarkaken usuli Sayyidina Waliyyul Asr (Allah ya gaggauta bayyanarsa).

Wasu daga cikin maganganun Ma'asumai (Alaihimus Salam) akan wannan batu sun hada da:

Imam Baƙir (A) — sa'ilin da yake bayyana addinin da Allah yake yarda da shi — bayan ya lissafa wasu abubuwa, sai ya ce:

«...وَالتَّسْلِیمُ لِاَمْرِنا وَالوَرَعُ وَالتَّواضُعُ وَاِنتِظارُ قائِمِنا...»

"...Da mika wuya ga al'amarinmu, da tsarguwa (nesantar zunubai), da kankan da kai, da kuma jiran Qa'im dinmu (mai tsayuwa da al'amari)..." (Al-Kafi, Juzu'i na 2, Shafi na 23) 

Imam Sadiƙ (A) ya ce:

 «عَلَیْکُمْ بِالتَّسْلیمِ وَالرَّدِّ اِلینا وَاِنْتظارِ اَمْرِنا وَامْرِکُمْ وَفَرَجِنا وَفَرَجِکُم.»

"Ku saduda (ku mika wuya), ku mayar da al'amura gare mu, kuma ku jira al'amarinmu da al'amarinku, da kuma saukinmu (samun mafita) da saukinku." (Rijal kashi, Shafi na 138)

Daga hadisan jiran bayyanar Imam Mahadi (Allah ya gaggauta bayyanarsa), za a gano cewa jiran bayyanar tasa ba wai kawai hanya ce ta kaiwa ga al'ummar da aka yi alkawarinta ba, a'a, shi kansa wannan jiran yana da matsayi na musamman (yana da lada mai zaman kansa). Ma'ana, idan mutum ya kasance yana rayuwa cikin ingantaccen jira, babu bambanci tsakanin ko ya riski abin da yake jiran ko bai riske shi ba.

Akan wannan dabi'a, wani mutum ya tambayi Imam Sadiƙ (A) cewa:

«مَا تَقُولُ فِیمَنْ مَاتَ عَلَی هَذَا اَلْأَمْرِ مُنْتَظِراً لَهُ؟»

"Me za ka ce game da mutumin da yake kan wannan al'amari (soyayya da bin shugabanni (Ahlul Baiti)) kuma yake jiran bayyanar gwamnatin gaskiya, sai ya rasu yana cikin wannan hali?"

Sai Imam (A) ya ba shi amsa da cewa:

«هُوَ بِمَنزِلَةِ مَنْ کانَ مَعَ القائِمِ فِیمَنْ فُسطاطِهِ». ثُمَ سَکَتَ هَنیئةً، ثُمَ قالَ: «هُوَ کَمَنْ کانَ مَعَ رُسولِ اللّه.»

"Yana a matsayin wanda yake tare da Qa'im (Imam Mahadi) ne a cikin tantinsa". Sannan ya yi shiru na dan lokaci, sannan ya ce: "Yana daidai da wanda ya kasance tare da Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da aliyansa) a cikin yakokinsa (yake-yakensa)." (Biharul Anwar, Juzu'i na 52, Shafi na 125)

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ciro daga littafin "Darsnameh Mahdaviyat" (Littafin Darasin Mahdawiyya) na Khodamurad Salimiyan, tare da ɗan gyara kadan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha